Ofishin kare haƙƙi na MDD ya wallafa saƙo a dandalin X, wanda aka sani da Twitter a baya, game da harin Isra’ila kan sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia ranar Talata.
“Ganin yawan fararen hular da aka kashe da kuma girman ɓarnar da aka yi a sansanin Jabalia, muna da damuwa babba cewa wannan hari ne kan mai tsautsayi da zai iya zama laifin yaƙi,” a cewar hukumar kare haƙƙi ta MDD.
A jiya ne jiragen yaƙin Isra’ila suka kai munanan hare-hare kan sansanin da yamma.
Hotunan da aka ɗauka sun nuna mummunar ɓarnar da aka yi, inda bama-bamai suka haƙa ramuka kuma ɓaraguzai da ƙarafa suka zagaye wurin baki ɗaya.
Kusan mutum 100 aka kashe a harin, ciki har da ƙananan yara.
Isra’ila na cewa ta kashe wani babban kwamandan Hamas a sansanin tare da lalata hanyar ƙarƙashin ƙasa da ƙungiyar ke amfani da ita.
Ta kuma ce tana bincike kan rahotonnin “ɓarna da kuma kisan fararen hula da aka yi”.