Iran ta yi alƙawarin mayar da martani ga abin da ta kira harin Isra’ila wanda ya lalata ofishin jakadancinsa da ke Damascus babban birnin Syria.
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce Isra’ila za ta yi da na sanin kai harin, yayin da shugaba Ebrahim Raisi ya dage cewa dole za a ɗauki mataki.
Gidan talabijin na Iran ya ruwaito mutuwar dakarun juyin juya-hali bakwai har da janar-janar biyu da ƴan Syriya shida.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ba ta yi magana kan rahotannin da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito ba.
Sai dai wani babban jami’in gwamnatin Isra’ila ya faɗa wa Reuters cewa waɗanda aka kashe na da hannu a hare-hare da dama da aka kai kan gine-ginen Isra’ila da Amurka kuma suna da ƙudirin kai ƙarin hare-hare.
Sun kuma bayyana cewa ba ofishin jakadancin aka nufa da harin ba. In ji BBC.
Jaridar New York Times ta ruwaito jami’an Isra’ila huɗu suna tabbatar da cewa Isra’ila ta kai harin tare da musanta cewa ginin ofishin jakadanci ne.
Isra’ila ta tabbatar da kai ɗaruruwan hare-hare a shekarun baya-bayan nan kan cibiyoyi a Syriya da ta ce suna da alaƙa da Iran da ƙungiyoyin mayaƙa da suke samun tallafin dakarun juyin-juya hali.