Kungiyar agaji ta Falasɗinawa ta Red Crescent ta ce sojojin Isra’ila sun zafafa hare-hare a kewayen asibitin Al-Quds da ke birnin Gaza.
Ƙungiyar ta wallafa sako a shafukan sada zumunta da ke cewa ana ci gaba da luguden wuta da harba makaman atilare a yankin.
Isra’ila ta ce ta zafafa hare-harenta a yankin ne domin tarwatsa Hamas da ke iko da Zirin Gaza.
Tana ci gaba da nanata gargaɗinta ga fararen hula, na su fice daga asibitin da sauran gine-gine.
Sai dai ma’aikatan lafiya da na agaji na cewa ba su da mafita a yanzu.
A wani hari na daban kuma sojojin Isra’ila sun lalata wani gini da suka ce na Hezbollah ne a cikin Lebanon.