Isra’ila ta shiga rana ta biyu wajen kai sabbin hare-haren a Zirin Gaza, inda rahotanni ke cewa ana ganin baƙin hayaki a sararin samaniyar yankin.
Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ya ce a yanzu suna kai wa Hamas hari ta ko’ina a zirin Gaza.
Wasu rahotanni da suka fito a daren jiya Juma’a daga Khan Yunis a kudancin Gaza na cewa munanan hare-hare sun tsananta a yankin.
Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce an kashe mutum fiye da 180 a hare-hare ta saman da aka kai a jiya Juma’a.
Majalisar Dinkin Duniya ta sake gargaɗi a kan taba fararen hula.


