Falasɗinawa sun fara azumin Ramadan yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a yankin tsakanin dakarun Isra’ila da sojojin Hamas kuma babu wata alamar cewa za a cimma tsagaita wuta.
Isra’ila ta lalata muhallan akasarin al’ummar Gaza, yayin da a alokaci guda hukumomin bayar da agaji ke gargaɗin cewa mutane za su mutu saboda yunwa.
A daren da ya gabata an yi artabu bayan da ƴansandan Isra’ila suka hana ɗarurtuwan matasa Falasɗinawa shiga masallacin Al Aqsa.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu dai ya sha alwashin ci gaba da ruwan wuta a birnin Rafah da ke kudancin Gaza duk da gargaɗin da shugaban Amurka Joe Biden ya yi kan batun.
A cikin saƙonsa na Ramadan ga al’ummar Gaza, Biden ya ce Musulmai da dama a duniya za su yi azumi ne da Falasɗinawa a ransu.