Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan yadda wani harin da ƙungiyar Hezbullah ta kai wani sansanin soji da ke arewacin ƙasar ya kashe sojoji huɗu tare da raunata wasu mutane 60.
Yana daya daga cikin manyan hare-hare da aka kai Isra’ila tun ɓarkewar rikici tsakanin ɓangarorin biyu shekara guda da ta gabata.
Hezbollah ta ce tana mayar da martani ne kan munanan hare-haren da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon da kuma Beirut.
A wata sanarwa da ta fitar ƙungiyar ta yi barazanar ci gaba da kai hare-hare matukar Isra’ila ta daina kai hare-hare a Lebanon ba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu.