Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana bincike domin tabbtar da raɗe-raɗin kisan jagoran ƙungiyar Hamas, Yahya Sinwar a Gaza.
Sanarwar da rundunar sojin Isra’ilan ta fitar ta ce har yanzu ba a gama tantance ko su waye ”Ƴan ta’adda uku” da dakarun suka kashe ba.
“Akwai ƴan ta’adda da aka kashe a cikin wani gini, kuma babu alamar akwai mutanen da aka yi garkuwa da su a cikin ginin.” inji sanarwar.