Hankali ya karkata ga Isra’ila kan yadda za ta mayar da martani kan harin jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da Iran ta kai mata sai dai ƙawayenta sun buƙaci ƙasar da ta guji ɓarkewar rikici.
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce Isra’ila ta yi nasara a faɗanta da Iran kuma dole ne a kaucewa rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya nemi a kwantar da hankali inda ya ce ƙasarsa za ta yi duk mai yiwuwa don hana ɓarkewar rikici.
Tun farko kuma sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Cameron ya shaida wa BBC cewa yana tunanin Isra’ila tana da hujja ta mayar wa Iran martani sai dai ya buƙaci ƙasar ta yi taka tsan-tsan ta kuma yi tunani a kai.