Isra’ila da Hamas sun tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi, inda Hamas za ta sako ‘yan Isra’ila 50 da take garkuwa da su, dukkansu mata da kananan yara.
Cikin wata sanarwar da Hamas ta fitar, ta yi ƙarin bayani kan cewa Isra’ila za ta saki Falasɗinawa matasa da mata 150 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.
Wakiliyar BBC ta ce jami’an Isra’ila sun ce an cimma yarjejeniyar dakatar da wuta ta kwanaki huɗu.
A tsakanin kwanakin ne za a miƙa Isra’ilawa 50, idan komai ya tafi daidai za a tsawaita dakatar da buɗe wutar da ƙarin kwanaki uku.
Qatar – wadda ta shiga tsakani – ta ce nan da sa’o’i 24 za a sanar da lokacin fara aikin yarjejeniyar.