Isra’ila da Amurka sun yi Allah-wadai da matakin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke shirin ɗauka na amincewa da kafa ƙasar Falasdinawa a watan Satumba mai zuwa.
Faransa ita ce ƙasa ta farko cikin ƙasashen G7 – ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya – da za ta fito fili ta bayyana matsayinta na goyon bayan kafa ƙasar Falasdinawa.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa wannan mataki na Macron yana da haɗari, yana mai cewa Hamas za ta yi amfani da shi wajen yaɗa farfaganda.
Haka zalika firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce wannan mataki tamkar ƙarfafa ayyukan ‘yan ta’adda ne.
Sai dai ƙasar Saudiyya ta yabawa shirin shugaban Faransa, tana mai cewa Macron ya kafa tarihi da wannan mataki.
Mahukuntan Falasdinu da ƙungiyar Hamas ma sun nuna gamsuwa tare da maraba da wannan yunkuri.