Rundunar sojin Isra’ila, ta ce burin firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu, na kawo ƙarshen ƙungiyar Hamas, ba abu ne mai yiwuwa ba.
A cikin wani jawabi ta talabijin, mai magana da yawun rundunar Rear Admiral Daniel Hagari, ya ce Hamas, aƙida ce, don haka ba aba ce da za a iya kawarwa ba.
Ya ce duk wanda ya yi muku wani alƙawari da ya saba wa wannan, yaudara ce kawai, Hamas ba aba ce da za a shafewa daga doron kasa ba.
Jim kaɗan bayan kalaman ne ofishin Firaministan Benjamin Netanyahu ya mayar da martani da cewa, abin da yake nufi shi ne lalata ƙarfin soji da ikon gudanar da mulki da ƙungiyar ke da shi. In ji BBC.
Daga baya kakakin sojojin ya sake fitar da sanawar, inda ya ce suna aiki a kan hakan.