Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar ƙungiyar Newcastle domin komawa Liverpool da taka leda a kakar baɗi.
BBC Sport ta kalato daga majiyoyi da dama cewa ɗanwasan ɗan asalin ƙasar Sweden ya riga ya ƙudurci burin komawa Liverpool kafin kakar baɗi kafin a rufe kasuwar hada-hadar ƴanwasanni a ranar 1 ga Satumba.
Tun da farko dai ƙungiyar Newcastle ta ƙi amincewa da tayin fam miliyan 110, lamarin da ya sa Liverpool ta yi barazanar ficewa da zawarcin ɗanwasan.
Kocin ƙungiyar, Eddie Howe ya bayyana cewa, “mun fahimci cewa Isak ya fi sha’awar tafiya wata ƙungiyar,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa ba zai ƙirga shi a cikin ƴanwasansa ba.
Ana dai sa ran Isak ba zai buga wasan farko na ƙungiyar, wanda za ta kara da Aston Villa ba a ranar Asabar mai zuwa.