Ƙasar Ireland ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda ta bi sawun Sifaniya da Norway, waɗanda suka yi hakan a safiyar yau.
“Gwamnati ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ‘yanci da kuma cin gashin kanta, kuma mun yarda za mu ƙulla alaƙar difilomasiyya tsakanin Dublin da Ramallah,” a cewar wata sanarwa.
Za a tura jakadan Ireland zuwa Falasɗinu “tare da cikakken Ofishin Jakadancin Ireland a Ramallah,” in ji sanarwar.
Ita ma Norway ta yabi matakin da ta ɗauka a matsayin “rana ta musamman”, inda Ministan Harkokin Waje Espen Barth Eide ya ce ƙasarsa na cikin waɗanda suka fi goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa sama da shekara 30″.
“Irin wannan rana da Norway ta amince da ƙasar Falasɗinawa a hukumance ta musamman ce a alaƙar ƙasashen,” a cewar Eide, yana mai cewa “abin takaici ne yadda gwamnatin Isra’ila ta gaza wajen nuna kyakkyawar niyya” wajen cimma ƙasa biyu.
Sifaniya kuwa ta amince da Falasɗinu ne bayan majalisar ministoci ta amince da hakan, in ji mai magana da yawun gwamnatin ƙasar.
Pilar Alegria ta ƙara da cewa majalisar “ta amince da mataki mai muhimmanci na amincewa da ƙasar Falasɗinu, wanda ke da manufa ɗaya tilo: don taimaka wa yunƙurin zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra’ila”.
Firaministan Sifaniya Pedro Sanchez ya faɗa kafin ya gana da majalisar tasa cewa “amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba abin tarihi ba ne kawai…sharaɗi ne na cimma zaman lafiya”.
Firaministan Ireland Simon Harris ya ce kafa ƙasa biyu ta Isra’ila da Falasɗinawa “ita ce hanya ɗaya da Isra’ila da Falasɗinawa za su rayu kafaɗa da kafaɗa cikin aminci”.
Da safiyar yau Talata ya ce akwai wani sabon salo “abin ƙyama kuma maras daɗin ji” inda Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kwatanta kisan Falasɗinawa da “‘tsautsayi'”.
Harris na magana ne kan harin Isra’ila a sansanin gudun hijira da ya kashe aƙalla mutum 45 ranar Lahadi. In ji BBC.