Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane uku da ta ce ta samu da safarar miyagun kwayoyi.
Mutanen na daga cikin daruruwan mutanen da ta rataye a kasar tun farkon shekarar nan ta 2023.
Shafin intanet na ma’aikatar shari’ar kasar, ya ce an rataye mutanen ne bayan da aka kama su da safarar hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogoram kusan 40.
An rataye mutane fiye da 200 a Iran a cikin shekarar nan saboda kama su da laifukan da suka jibanci safarar muggan kwayoyi da kuma zanga-zangar kin jinin gwamnati.
Kungiyoyin kare hakkin dan’Adam sun ce a yanzu Iran ta fi sauran kasashen duniya zartar da hukuncin kisa bayan China. In ji BBC.