Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce, Iran za ta ɗandana kuɗarta bayan hare-haren da ta kai a birnin Tel Aviv a ranar Talata.
Sai dai rahotanni daga Tel Aviv na nuna cewa yawancin makamai masu linzamin guda 180 da Iran ta harba, Isra’ila ta kakkaɓo, amma an kashe wani Bafalasɗine guda ɗaya a gaɓar yamma da tekun Jordan, sannan hare-haren sun kai ga wata makaranta da wajen cin abinci a birnin na Tel Aviv.
A nata ɓangaren, Iran ta ce ƙaddamar da hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila, ciki har da kashe jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah.
Haka kuma Isra’ila ta ce za ta cigaba da kutsawa cikin ta ƙasar kamar yadda ta fara, a daidai lokacin a Hezbollah ɗin ta ce ta dakatar da dakarun Isra’ila ɗin shigowa yankinta.


