Wani ɗan majalisar yaƙin Isra’ila, Benny Gantz, ya ce ƙasar Iran za ta ɗanɗana kuɗarta dangane da harin da ta kai mata, kuma za ta mayar da martani a lokacin da ya dace.
Wata sanarwa da aka fitar a ba da daɗewa gabanin taron majalisar yaƙin Isra’ila Gantz ya ce: “Za mu gina haɗin gwiwa a yankin mu kuma Iran za ta ɗanɗana kuɗarta a lokacin da ya dace a gare mu.
“Kuma abu mafi mahimmanci, idan muka fuskanci muradin makiyanmu na cutar da mu, za mu ci gaba da haɗa kai da ƙara karfi.”
Gantz ya ce ya kammala tattaunawa da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock.
“Mun tattauna da farko game da wajibcin samar da haɗin kai a duniya don daƙile ta’addancin Iran kai-tsaye da kuma ta hanyar wakilanta – a yanki da kuma duniya,” in ji Gantz a wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta.