Hukumomi a Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane uku bisa alaƙa da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka gudanar a ƙasar a bara, kamar yadda ma`aikatar shari`a ta ƙasar ta bayyana.
An yanke wa mutanen uku hukuncin ne bisa zarginsu da hannu a harin da ya kashe jami`an tsaro uku a Isfahan, a watan Nuwamba.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty international ta ce, an yi musu shari`a ba bisa ƙa`ida ba tare da zargin an azabtar da su.
An rataye wasu ƴan zanga-zangar huɗu tun watan Disamba.
An bayar da rahoton cewa an yanke wa wasu da dama hukuncin kisa ko kuma an tuhume su da aikata manyan laifuka.
Zanga-zangar dai ta mamaye duk faɗin jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan mutuwar wata mata baƙurɗiya mai shekaru 22, Mahsa Amini, a hannun ƴan sanda bayan zargin ta da sanya hijabi ba daidai ba.
Mutanen uku da aka zartar wa hukunci a ranar juma`a- Majid Kazemi mai shekaru 30, da Saleh Mirhashemi mai shekaru 36, da kuma Saeed Yaqoubi mai shekaru 37- an kama su ne bayan zanga-zangar da aka yi a tsakiyar birnin Isfahan a ranar 16 ga watan Nuwamba, inda aka harbe wasu jami`an rundunar `yan sandan farin kaya ta Basij guda biyu tare da wani ɗan sanda.
Majiyoyi sun shaida ma ƙungiyar kare haƙƙin bil`adama cewa an tilasta wa mutanen amsa laifinsu ne, sannan aka azabtar da su tare da tilasta musu yin kalaman ɓatanci waɗanda suka zama tushen laifukan da ake tuhumarsu da su .
An yi zargin cewa masu yi musu tambayoyi sun ajiye Kazemi a kife, suka nuna masa faifan bidiyo na yadda suke azabtar da dan uwansa, inda suka yi masa kisan gilla tare da yi masa barazanar kashe sauran `yan uwansa.