Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin kisa sakamakon kama su da laifin aikata fyaɗe, kamar yadda kamfanin labarai na Mizan mai alaƙa da ma’akatar shari’a ya ruwaito.
An aiwatar da hukuncin ne da tsakar daren da ya gabata a wani gidan yari da ke birnin Gorgan.
Heidar Asiabi, shugaban sashen shari’a na lardin, ya ce an fara bincike ne bayan wata mace ta shigar da ƙorafin yin garkuwa da ita.
Bayan tsananta bincike ne kuma wasu matan uku suka fito da zargin aikata fyaɗe. “Saboda girma da kuma kamanceceniya wajen aikata laifin aka kafa wata tawaga ta musamman da ta ƙunshi alƙalai da jami’an tsaro,” in ji Asiabi.
Bayan gano gungun mutum ukun cikin gaggawa, an kai su kotu tare da yanke musu hukunci, inda ita ma kotun ƙoli ta amince da shi.
Iran ta zartar wa aƙalla mutum 901 hukuncin kisa a 2024 kaɗai, a cewar Volker Turk, shugaban hukumar kare haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya.