Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri.
Hukuma ta ce an kama Esmail Fekri a shekarar 2023, kuma yana ƙoƙarin miƙa wa Isra’ila bayanan sirri ne don samun kuɗi.
Wannan ne karo na uku a baya-baya nan da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa saboda zargin leƙen asiri ga Isra’ila.
A ranar Lahadi, Isra’ila ta ce ta kama wasu ‘yan ƙasa biyu da ake zargin suna aiki da hukumar leƙen asirin Iran.
Babban alƙalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya bayyana a ranar Litinin cewa, la’akari da yanayin “yaƙi” da suke ciki, dole ne a gudanar da shari’o’i ga waɗanda ake zargin suna aiki da Isra’ila cikin hanzari.