Iran ta zartar da hukuncin kan wani ɗan Sweeden da ke da takardar zama ɗan iran kan zarginsa da hannu a wani hari da aka kai kan sojoji a 2018, lokacin da suke fareti.
Habib Chaab shi ne ya ƙirƙiri kungiyar mayaƙa ta Larabawa da ke neman ‘yanci a lardin Khuzestan a kudu maso yammacin Iran.
Ya shafe shekara 10 yana gudun hijira a Sweeden lokacin da wani jami’in leken asiri na Iran ya sace shi a Turkiyya a 2020.
Ministan harkokin wajen na Sweeden Tobias Billstrom ya ce gwamnatinsu ta shawarci Iran da kada ta zartar masa da wannan hukunci.
“Hukuncin kisa bai dace ba rashin hankali ne kuma Sweeden da sauran ƙasashen Tarayyar Turai sun yi Allah-wadai da wannan hukunci,” in ji shi.
Kotun Iran ta zargi Chaab da shugabantar Harakat al-Nidal ko Ahvaz Arab, wadda iran ta ce ƙungiyar ‘yan ta’addace da ke kai hare-hare a ƙasar.