fidelitybank

Iran ta nuna irin karfin da take da shi a lokacin da ta kai wa Isra’ila hari – Khamenei

Date:

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ali Ayatullah Khamenei ya ce, kasarsa ta nuna irin karfin da take da shi a lokacin harin da aka kai wa Isra’ila, ba tare da la’akari da adadin da aka kai mata hari ba.

Makwanni biyu da suka gabata Iran ta harba jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami kan Isra’ila a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai ofishin jakadancinta a Damascus na kasar Siriya a ranar 1 ga Afrilu.

Amma yawancin jirage marasa matuka da makamai masu linzami tsarin tsaron Isra’ila ne ya kame su.

Duk da haka, Khamenei ya yabawa Sojojin Iran da suka kai wa Isra’ila hari.

Da yake magana a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce: “Nawa ne makami mai linzami da aka harba, kuma nawa ne aka harba musu, ba ita ce tambaya ta farko ba, abin da ke da muhimmanci shi ne Iran ta nuna karfinta a yayin wannan farmakin.

Khamenei ya kara da cewa, “A cikin farmakin na baya-bayan nan, sojojin sun yi nasarar rage tsadar kayayyaki tare da kara samun nasarori,” in ji Khamenei, yana mai kira ga jami’an soji da su ci gaba da bin sabbin hanyoyin soja tare da koyan dabarun abokan gaba.

Amma, da sanyin safiyar Juma’a, wasu fashe-fashe sun mamaye birnin Isfahan na kasar Iran, lamarin da da dama suka yi imanin cewa harin ramuwar gayya ne daga Isra’ila.

news today in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp