Kasar Iran ta yi kira ga Saudiyya da ta saki daya daga cikin ƴan kasarta da aka kama a lokacin aikin Hajji, yayin da kasashen biyu da ke takaddama da juna suka soma dinƙe ɓarakar da ke tsakaninsu.
A wata sanarwa Jamhuriyar ta Musulunci ta bayyana cewa an tsare dan ƙasarta dangane da wata wayar tarho tsakanin ministan harkokin waje Hossein Amir-Abdollahian da takwaransa na Iraq Fuad Hussein.
Iraki ta cigaba da shiga tsakani domin sulhunta Saudiyya da Iran tun watan Afrilun shekarar da ta gabata.
“A wayar, ministan harkokin wajen Iran ya yi bin sawu kan makomar dan Iran da aka tsare a Saudiyya lokacin aikin Hajji kuma ya yi ba da saƙon kira a sako shi,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ba ta ba da ƙarin bayani a kan sunan wanda aka tsare ko dalilin tsare shi a lokacin aikin Hajji da aka yi a watan da ya gabata ba. Kimanin mutane 780,000 ne suka yi aikin Hajjin wannan shekara kamar yadda jami’an Saudiyya suka bayyana. In ji BBC.


