Rundunar sojin Isra’ila ta ce Iran ta kaddamar mata da hare-hare masu linzami.
Sanarwar da rundunar sojin Isra’ila ta fitar ta ce hare-haren sun fito ne daga Iran.
Iran ta tabbatar da kaddamar da hare-haren kan Isra’ila, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar IRNA ya tabbatar.
Isra’ila ta bukaci ƴan ƙasarta su kasance cikin shiri tare da neman wurin fakewa idan har sun ji ƙara ta gargaɗi.
Masu aiko da rahotanni sun ce an kakkaɓo wasu makaman a sararin samaniyar Jordan.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce harin makamai masu linzami kusan 100 Iran ta harbo.
Sai dai rahotanni sun ce Amurka ta taimaka wa Isra’ila wajen kakkaɓo makaman kafin isa Tel Aviv.
Bayanai sun ce wasu makaman da Iran ta harbo sun faɗa yankunan Falasɗinawa


