Iran ta ce idan muka fara buɗe biranen makamai a kullum tsawon shekara biyu ba za mu gama ba har nan da shekara biyu.
Da irin wannan kalaman Iran ta fara bayyana wasu jerin unguwanni na ƙarƙashin ƙasa da ke ɗauke da makamanta masu linzami da za ta yi amfani da su wajen abin da ta bayyana a matsayin ramuwar hare-hare kan Isra’ila da Amurka.
An ce Amurka ta fara tura jiragen yaƙinta shida a makon da ya gabata masu ƙarfin kai hari da manyan bamabamai a Iran da Yemen, kamar yadda wasu majiyoyi suka faɗa wa kamfanin klabarai na Reuters.