Ministan harkokin waje na Iran ya amince an yi wa tashoshin nukiliyar ƙasarsa abin da ya kira gagarumar ɓarna a hare-haren baya-bayan nan da Amurka da Isra’ila suka kai.
Abbas Araghchi ya ce hukumar kula da makaman nukiliya a ƙasar na gudanar da bincike.
Kalamansa na zuwa ne yayin da Washington ke ci gaba da jaddada cewa hare-haren da ta kai sun kassara burin Iran kan nukiliya.
Manyan jami’an gwamnatin Amurka sun yi jawabi ga ƴan majalisar dattawan ƙasar. Ƴan Republicans sun ce a bayyane take ƙarara cewa an yi nasara a hare-haren sai dai wani ɗan Democrat guda, Chris Murphy ya ce abu ne mai wuya a iya rusa ilimi.