Shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce, Iran da ƙawayenta ba su jin tsoron yin fito na fito da Isra’ila, duk da kashe shugabannin Hamas da Hizbollah da Isra’ilar ta yi.
Ayatollah Khamenei ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da hudubar Juma’a a babban massalacin Tehran, inda ya ce harin da Iran din ta kai wa Isra’ila halastacce ne kuma ɗan ƙaramin hukunci ne na laifukan da Isra’ilar take aikatawa.
Ya ce, “me ya kamata mu yi ? daga ɓangaren ƴan siyasa da dakarun soji da kuma sauran hukumomi, duk za mu hadu mu dauki matakin da ya dace, a lokacin da ya dace kamar dai yadda muka saba yi a baya.”
Shugaban addinin ya kuma yi wa shugaban Hizbollah da aka kashe Hassan Nasrullah addu’a tare da jinjina masa.
Ministan harakokin wajen Abbas Araghchi ya isa Lebanon domin ganawa da shugaban siyasar ƙasar.
Wannan ne karon farko da jagoran addunin na Iran ya yi huɗubar Juma’a, tun bayan kisan da Amurka ta yi wa kwamandan dakarun juyin juya hali Qassem Soleimani a Janairun 2020.