fidelitybank

IPOB ‘yan ta’adda ne – Birtaniya

Date:

Gwamnatin Birtaniya ta bi sahun ta Najeriya wajen ayyana ƙungiyar ‘yan aware masu neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriyar a matsayin ta ‘yan ta’adda.

Hakan na nufin Birtaniya ba za ta bai wa mambobin ƙungiyar mafaka ba kamar yadda ta yi niyya a baya. A cewar BBC.

Tun a 2017 ne gwamnatin Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin ta ‘yan ta’adda saboda kashe-kashen da hukumomi ke zargin ta da aikatawa a jihohin kudu maso gabashin ƙasar da suka haɗa da Anambra, da Abia, da Ebonyi, da Imo, da Enugu.

Matakin na ƙunshe ne cikin kundin ayyukan hukumar harkokin cikin gida ta Birtaniya, inda ta ce ƙungiyar “yan ta’adda ce sakamakon ayyukan tashin hankali da take aikatawa”.

Lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin Najeriya ta ce IPOB ce ta kashe wasu sojojinta biyu mace da namiji da ke shirin yin aure a Jihar Imo da ke yankin na kudu maso gabas. Sai dai ƙungiyar ta musanta zargin.

Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da Nnamdi Kanu shugaban ƙungiyar, wanda ke da shaidar zama ɗan ƙasar Birtaniya a gaban kotu, tana mai zargin sa da haddasa tashin hankali da raba kan ‘yan ƙasa.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp