fidelitybank

IPOB ce ta 10 a jerin kungiyoyin ta’addanci a duniya – Rahoto

Date:

Haramtacciyar ƙungiyar ƴan a-ware ta Biafra, (IPOB) da ke kudancin Najeriya ta zama ta goma a cikin ƙungiyoyin da suka fi aikata ta’addanci a duniya.

Wata ƙididdiga da rahoto (Global Terrorism Index (GTI) na wannan shekara ta 2023 da aka fitar na duniya game da ta’addanci wanda ya sanya ƙungiyar a wannan mataki, ya ce hare-hare 40 da kisan gilla 57 da ta aikata a 2022 su suka sa ta kai wannan mataki.

Daga cikin kisan gillar da IPOB din ta aikata akwai na hallaka wasu sojojin Najeriya ango da amarya, wadanda ta gille musu kai, da kisan ‘yan arewacin kasar da ke kudu maso gabashi da kuma kisan jami’an tsaro da dama.

Karanta Wannan: ‘Yan IPOB ne suka zabi Obi a Legas – Biodun

Rahoton wanda ya bayyana ƙungiyar ta IPOB da cewa mai haɗarin gaske ce a ta’addanci, ya sanya Al-Shabaab a matsayin ta ɗaya a duniya wajen ta’addanci.

Ƙungiyar ta Al-Shabaab wadda take da ƙarfi a gabashin Afirka rahoton ya nuna cewa ta yi kisan gilla 784 da hare-hare 315, yayin da ƙungiyar IS ta lardin Khorasan (ISK) ta yi kisa 498 da kuma hare-hare 141.

Sai kuma ƙungiyar Jamaat Nusrat Al-Islam wal Muslimeen (JNIM), wadda ta hallaka rayuka 279 da kai hari 77, yayin da Balochistan Liberation Army (BLA), ta hallaka rai 233 ta kai hari 30.

Ita kuwa ƙungiyar IS ta yammacin Afirka (ISWAP), ta kasance ta 6 a rahoton inda ta hallaka rai 219 da kai hari 65, yayin da Boko Haram ke bi mata baya da kisan kai 204 da hare-hare 64. In ji BBC.

legit nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp