Kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa (IPMAN), ta yi barazanar gurfanar da mahukuntan Hukumar Kula da Man Fetur ta kasa (NMDPRA) a gaban Kotu, saboda ikirarin da ta yi na biyan Naira Biliyan 74 na kudin jigilar kayayyaki ga ‘yan kasuwa.
A ranar Laraba 29 ga watan Yulin 2022 ne hukumar NMDPRA ta bayyana cewa ta biya ‘yan kasuwa Naira biliyan 74 a cikin watanni bakwai da suka gabata.
Shugaban kungiyar IPMAN ta Arewa, Bashir Danmalam ya yi wannan barazanar lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano
Danmalam ya ce maganar ba gaskiya ba ce domin ba a biya mambobinsu sai dai idan an biya ‘yan kasuwar fatalwa.
Shugaban na IPMAN ya kalubalanci mahukuntan NMDPRA da su fito da sunayen duk ‘yan kasuwar da aka biya domin tabbatar da ikirarin su.
“Na yi mamakin jin labarin biyan Naira biliyan 74 da Shugaban Hukumar Faruk Ahmed Maishanu ya yi. Ko dai an ba shi labari ne ko kuma bai san abin da ke faruwa a wurin ba.
“Wa kuma wa aka biya kudin? Na san wasu ’yan kasuwa da ake bin su bashin Naira biliyan 10 kowanne. Don haka a ce hukumar ta biya Naira biliyan 74 ga ‘yan kasuwa ba gaskiya ba ne.
“Don haka, za mu iya yarda da biyan kuɗin da aka ce kawai idan an biya kuɗin ga”‘ yan kasuwa na fatalwa” ko kuma idan wani ɓangare ne na takardar da aka ƙi.
“Ya kamata gwamnatin tarayya ta sallami wannan mutumi saboda bai cancanta ya rike irin wannan mukami ba ganin cewa bai san abin da ke faruwa a can ba,” inji shi.
Ya yi nuni da cewa gazawar hukumar wajen sasanta ikirari na sufurin ‘yan kasuwar da ya kai kimanin Naira biliyan 500 ne ya janyo karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan.
Danmalam ya ce, bisa binciken da kungiyar IPMAN ta gudanar, an gano cewa a baya-bayan nan ne hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa (NNPC) ta saki sama da Naira biliyan 70 ga hukumar domin biyan ‘yan kasuwar da har yanzu ba a biya su ba.
Ya koka da cewa kafin yanzu ana biyan mambobinsu kudadensu a cikin wata daya ko biyu sabanin yadda ake biyansu a halin yanzu.