Wasu ɓata gari da ba a san ko su waye ba, sun yi wa wani ƙaramin yaro Junaidu Ibrahim dan shekaru 7 yankan Rago a garin Zangon Dan Abdu da ke Karamar Hukumar Rimingado a Kano.
Mahaifin yaron Ibrahim Aliyu ya shaida wa Arewa Updates cewa, a ranar Lahadi yana zaune aka zo aka sanar da shi an ga yaronsa an fasa masa kai a gona, amma da ya je sai ya tarar an yi masa yankan rago ne.
Shi ma mai unguwar yankin Ibrahim Chiroma ya ce, sun binciki yaron ba a cire komai na jikinsa ba, amma suna zargin ɓata garin jininsa suka tatsa.
A wani mai kama da wannan, ranar Asabar wasu ɓata gari sun rataye wata yarinya Fatima Sule ƴar shekaru 13 a jikin taga a unguwar Dandishe Yamma layin Malam Kamalu da ke Karamar Hukumar Dala a Kanon.
Rahotonnin da Arewa Updates ta samu sun nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da mahaifiyar yarinyar ta tafi unguwa, amma da dawowarta ta tarar da ita rataye a mace.