Rundunar ‘yan sanda a Legas ta kama wani injiniyan farar hula da ke kula da aikin da wata tankar ruwa ta fado ta kashe mutane biyu a ranar Lahadi.
Jami’in hulda da jama’a, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kamun ranar Talata.
Kakakin ya shawarci jama’a da su guji amfani da injiniyoyin da basu cancanta ba.
“Wata tankar ruwa da ake gyarawa ta fado a saman rufin wani gini da ke kusa, inda nan take ta kashe ‘yan uwa biyu, inda mahaifiyarsu da wani mutum guda suka jikkata.
“Injiniya yana hannunmu. Ana ci gaba da gudanar da bincike,” Hundeyin ya kara da cewa.
Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a Kudu maso Yamma, ya ce lamarin ya faru ne a Ladi Lak, a yankin Bariga da ke Legas.
Jami’in ya shaida wa NAN cewa tankin ya fado ne daga wani bene mai hawa biyu zuwa wani bungalow mai makwabtaka da shi, inda ya yi sanadin mutuwar wani babba namiji da yaro.


