Tawagar Italiya za ta kara da ta Ingila a wasan neman gurbin shiga gasar nahiyar Turai ranar Alhamis a filin wasa na Diego Maradona.
Tawagogin sun fafata a kakar nan, inda suka tashi 0-0 ranar 11 ga watan Yunin 2022 a Wembley a karawar Nations League.
A wasa na biyu kuwa ranar 23 ga watan Satumabar 2022, Italiya ce ta ci 1-0 a dai Nations League.
Tun kan nan Italiya ta doke Ingila ta lashe kofin nahiyar Turai a Wembley a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1.
Harry Kane na fatan zama kan gaba a yawan cin kwallaye a tawagar Ingila, zai haura Wayne Rooney.
Kane, wanda kawo yanzu ya ci wa Ingila kwallo 53, kenan ya yi kan-kan-kan da Rooney.
Wannan shine wasan farko da Ingila za ta buga tun bayan gasar kofin duniya, wadda Faransa ta fitar da Ingila a quarter finals.
Ita kuwa Italiya ba ta je wasannin da aka yi Qatar ba, bayan da ta kasa samun gurbi.