Najeriya ba za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe ba a gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA da ke gudana a Australia da New Zealand.
Hakan na zuwa ne bayan Super Falcons ta sha kashi a hannun Ingila a bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagaye na 16 a ranar Litinin da ci 3-1.
Najeriya ta buga kunnen doki 0-0 da Ingila bayan mintuna 120.
Desire Oparanozie da Michelle Alozie sun yi rashin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Za a yi wasannin daf da na kusa da na karshe ne a ranar Juma’a da Asabar.