An saka dan wasan tsakiya na Leicester James Maddison a cikin ‘yan wasa 26 da Ingila za ta wakilci kasar a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.
Mai horaswa Gareth Southgate, ya kuma zabo dan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford da dan wasan Newcastle Callum Wilson da dan wasan baya na Manchester City Kyle Walker da kuma dan bayan Arsenal Ben White.
Amma dan wasan baya na AC Milan Fikayo Tomori da dan wasan Brentford Ivan Toney da dan wasan gaba na West Ham Jarrod Bowen ba su samu ba.
Ingila za ta kara da Iran a gasar cin kofin duniya ranar 21 ga watan Nuwamba agogon (13:00 GMT).
Wales da Amurka ne ke hade da su a rukunin B.
Dan wasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips, duk da cewa ya dawo daga hutun watanni biyu yana fama da matsalar kafadarsa, hakama Harry Maguire na tsakiya, wanda yasha wahala wajen samun wasa a Manchester United a kakar wasa ta bana.
Sai dai abokin wasan Maguire Jadon Sancho bai shiga cikin tawagar ba.
Zabi tawagar ku ta Ingila a gasar cin kofin duniya
Shearer ya yi hasashen fitar Ingila wasan daf da na kusa da karshe
tawagar Ingila
Masu tsaron gida: Jordan Pickford (Everton), Nick Pope (Newcastle), Aaron Ramsdale (Arsenal)
Masu tsaron baya: Harry Maguire (Manchester United), Luke Shaw (Manchester United), Eric Dier (Tottenham), John Stones (Manchester City), Kyle Walker (Manchester City), Kieran Trippier (Newcastle), Conor Coady (Everton), Ben White (Arsenal), Trent Alexander-Arnold (Liverpool)
‘Yan wasan tsakiya: Jude Bellingham (Borussia Dortmund), Mason Mount (Chelsea), Conor Gallagher (Chelsea), Declan Rice (West Ham), Jordan Henderson (Liverpool), Kalvin Phillips (Manchester City)
‘Yan wasan gaba: James Maddison (Leicester), Phil Foden (Manchester City), Jack Grealish (Manchester City), Harry Kane (Tottenham), Bukayo Saka (Arsenal), Raheem Sterling (Chelsea), Callum Wilson (Newcastle), Marcus Rashford (Manchester). United)