fidelitybank

Inganta albashin ‘Yan sanda: Majalisa ta amince da karin albashin su

Date:

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da sake duba tare da inganta albashin ‘yan sanda da kashi 20 cikin 100.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, bayan kammala taron majalisar zartarwa na tarayya wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranta a sabbin zaurukan majalisar da a ka yi wa kwaskwarima.

A cewar ministan,”A na sa ran aikin bitar zai fara aiki daga watan Janairun 2022. Wannan bita ya biyo bayan bukatun da masu zanga-zangar EndSARS su ka gabatar a shekarar 2020, wanda ya shafi inganta jin dadin jami’an ‘yan sanda”.

Ya ci gaba da cewa,”Za a kara albashin daukar gida ne ta hanyar alawus din yawon bude ido zuwa kashi 6 cikin 100 na sabon albashin da za su tafi gida da kuma amincewa da Naira biliyan 1.12 domin biyan wasu fa’idodin da ba su da inshora a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2020”. Inji Maigari.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa za a inganta albashin daidai da yadda a ke yi domin ci gaba da wanzar da zaman lafiya a kasar.

Zauren majalisar ya kuma amince da fitar da Naira biliyan 13.1 donmi biyan wasu fa’idodin mutuwa na ma’aikata 5,472 na tsawon lokacin rashin inshora na 2013 zuwa Agusta 2021.

 

nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp