A shirye-shiryen da take yi gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana shirin ta na fitar da ƙarin ƙa’idoji da za su jagoranci yadda za a duba sakamakon zaɓe da aka riga aka bayyana.
Shugaban INEC, farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a taron kwata na biyu da kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) a Abuja .
Ya jaddada cewa kwamishinonin zaɓe su ɗauki cikakken nauyin aikinsu bisa ƙundin tsarin mulki.
Farfesa Yakubu ya kuma bayyana damuwa kan yadda mutane ke fassara Sashe na 65 na dokar zaɓe ta 2022 .wadda ke ba INEC damar duba sakamakon zaɓe ta hanyoyi daban-daban, inda ya ce hukumar na aiki kan sabbin ƙa’idoji da za su bayyana yadda ake nazari da sake duba sakamakon zaɓe.
“Sabbin dokokin za su kasance ƙari ne ga dokokin gudanar da zaɓe na 2022, kuma za a wallafa su a shafin hukumar nan bada jimawa.” shugaban hukumar ya ƙara da cewa.
Ya kara da cewa INEC ta riga ta gana da shugabannin jam’iyyu da ƙungiyoyin fararen hula da ‘yan jarida da jami’an tsaro domin samun haɗin kai.
Haka kuma, dukkan jihohin Najeriya da Abuja sun riga suna da sabbin kwamishinonin zaɓe (RECs) masu cikakken iko.