Hukumar zaɓe INEC a jihar Kogi, za ta fara zaman tattara sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar.
A cewar hukumomi, za a fara tattara sakamakon daga ƙananan hukumomi da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Lahadi.
‘Yan takara 18 ne suka fafata a zaɓen na jiya Asabar.
Kogi na da ƙananan hukumomi 21 kuma ana sa ran bayyana wanda ya lashe zaɓen nan da tsakar dare ko kuma safiyar Talata