Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka ranar Juma’a yayin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar kula da gidajen yari na ƙasar, Sylvester Ndidi Nwakuche Ofori, da ya buƙaci hakan.
Mista Ofori ya ce ya kamata hukumar ta duba wannan buƙata tasa saboda su ma ɗaurarru suna da ƴancin zaɓe a ƙarƙashin dokokin Najeriya.
“Kowa zai iya samun kansa a wannan yanayi, idan ya saɓa doka, don haka ya kamata mu duba yadda kula da su, suna da ƴancin da doka ta ba su, ɗaya daga cikin ƴancin kuwa shi ne ƴancin kaɗa ƙuri’a. Kasancewarsu a kurkuku ba zai janye musu ƴancinsu na zaɓe ba,” in ji Mista Ofori.
Shugaban hukumar kula da gidajen yarin ya ce akwai ɗaurarru fiye da 81,000 a faɗin gidajen yarin ƙasar, kuma kusan kashi 66 daga cikinsu na zaman jiran shari’a ne.
Hukunce-hukunce kotuna a 2014 da 2018 sun tabatar da hukuncin bai wa ɗaurarrau damar kaɗa ƙuri’unsu a zaɓukan ƙasar.
Shugaban hukumar zaɓenya ce INEC ta yi jerin ganawa da hukumar kula da gidajen yarin domin tsara yadda ɗaurarrun za su kaɗa ƙuri’ar tasu, ciki har da samun damar zuwa inda suke ɗaure domin ba su damar jefa ƙuri’a.
Haka kuma shugaban na INEC ya nemi ɗaukin majalisar dokokin ƙasar domin tabbatar da ƙudurin.