fidelitybank

INEC ta yi daidai da ta ayyana zaɓe bai kammalu ba a Adamawa – Binani

Date:

Ƴar takarar kujerar gwaman jihar Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin hukumar zaɓe INEC da ta ɗauka na bayyana zaɓen gwaman jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

Yayin da ta bayyana a cikin shirin ‘Politics Today’ na gidan talbijin ɗin Channels, Sanata Aishatu Binani, ta yi maraba da matakin, inda ta yi zargin cewa an aikata kura-kurai da rikice-rikice a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Muhammadu Mele na jami’ar Maiduguri ne ya ayyana sakamakon zaɓen gwaman jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwaman jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ke neman wa’adin mulkin jihar karo na biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 421,524, yayin da ita kuma Sanata Binani ta jam’iyyar APC ke da yawan ƙuri’u 390,275.

Jami’in zaɓen ya bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 69 a faɗin jihar ba, kuma adadin katunan zaɓen da aka karɓa a duka rumfunan sun kai 37,016, wanda kuma adadinsu ya zarta tazarar ƙuri’u 31,249 da ke tsakanin ‘yan takarar biyu.

Sanata Aishatu ta ce, ”matsayina game da matakin shi ne jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar ya yi daidai da ya bayyana sakamakon zaɓen jihar a matsayin wanda bai kammala ba”

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp