Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta tabbatar da cewa sakamakon zaben 2023 ya nuna muradin al’umma.
Abubakar ya yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Paul Ibe ya fitar a Abuja ranar Alhamis a yayin bikin ranar dimokradiyya ta duniya.
Abubakar ya bukaci INEC da sauran hukumomin gwamnati da ke taka rawa a harkokin zabe da su tabbatar da cewa sakamakon zaben ya kasance mai nuna muradin al’umma.
Dan takarar shugaban kasa na PDP ya ce bikin dimokuradiyya, hakika, bikin ikon mutane ne.
Ya ce duk da cewa an samu ci gaba sosai a tsarin da aka gudanar da zabuka a Najeriya, “zaben 2023 wata dama ce ga INEC ta nuna cewa hukumar ta bunkasa fiye da bangaranci,” in ji shi.