fidelitybank

INEC ta tsayar da ranar Asabar a matsayin ranar ƙarasa zaɓe a wasu jihohi

Date:

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC, ta sanya Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙarasa zaɓukan da ba su kammala ba a jihohi da dama na ƙasar nan.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin, INEC ta ce, ta yanke wannan shawara ce, bayan wata ganawa tsakanin manyan jami’anta.

Akwai zaɓukan gwamnoni kamar a jihohin Kebbi da Adamawa, waɗanda jami’an sanar da sakamakon zaɓe suka ce ba su kammala ba a ranar 18 ga watan Maris, baya ga sauran zaɓukan ‘yan majalisun dokoki, da su ma suka fuskanci irin wannan cikas.

Ɗaya daga cikin jihohi da aka samu zaɓukan da ba su kammala ba masu yawa a ranar 25 ga watan Fabrairu, ita ce Sokoto, inda ake da ‘yan majalisar wakilai 11 da sanatoci 3 waɗanda duk zaɓensu bai kammalu ba.

Masu sa-ido sun soki hukumar INEC saboda matsalolin da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, wanda Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasarar zama sabon shugaban ƙasa.

Haka ma a ranar 18 ga watan Maris lokacin da INEC ta gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi, an gamu da wasu daga cikin matsalolin da aka samu a zaɓen INEC na farko

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...
X whatsapp