Hukumar zaɓe ta INEC, ta tsawaita wa’adin karɓar katin zaɓe da take rabawa a faɗin ƙasar da kwana takwas.
Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na Inec Festus Okoye ya ce an ɗauki matakin ne don bai wa masu kaɗa ƙuri’a isasshen lokaci na karɓar katin kafin fara jefa ƙuri’a a babban zaɓe na 2023.
“Saboda wannan dalilin, an tsawaita wa’adin karɓar katin zaɓen da kwana takwas,” in ji shi. “A madadin wa’adin ya ƙare ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu, za a ci gaba da karɓa har zuwa Lahadi, 29 ga wata.”
Inec ta ce lokacin karɓar katin shi ne 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a kowace rana – har Asabar da Lahadi.
Kazalika, tsawaitawar ta shafi dukkan matakan raba katin na ƙaramar hukumar da kuma mazaɓa.
A ranar 25 ga watan Fabarairu ne za a fara kaɗa ƙuri’a, inda ake sa ran ‘yan Najeriya miliyan 93.4 da ke da rajistar zaɓen za su zaɓi shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya. Sai kuma gwamnoni da ‘yan majalisar jiha da za a zaɓa a watan Maris.