fidelitybank

INEC ta tabbatar da hatsarin jirgin ruwa ga jami’an ta a jihar Bayelsa

Date:

 A jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya, hukumar zaɓe ta ƙasa National Independent Eloctoral Commission (INEC), ta tabbatar da hatsarin da wani jirgin ruwa ya yi lokacin da yake jigilar jami’anta.

Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa rumfar zaɓe ta 17 a Koluama da ke ƙaramar hukumar Ijawa ta kudu ɗauke da kayayyakin zaɓe masu muhimmanci.

Shugaban sashen wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a na Inec a jihar Bayelsa, Wilfred O. Ifodah, ya ce an ceto dukkan jami’ai 12 da ke cikin jirgin.

Sai dai ya ce akwai kayan aikin zaɓe da suka ɓace, waɗanda suka haɗa da takardar rubuta sakamakon zaɓe, da na’urorin cajin batirin kwamfutar aikin zaɓen, da kuma wasu kayyayakin.

Sanarwar da Inec ta fitar ta ce masu zaɓe 5,368 ne suka yi rijista a yankin, kuma 5,311 sun karɓi katin zaɓensu.

Inec ta ce tana bakin ƙoƙarinta don ganin an gudanar da zaɓe a yankin lami lafiya

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp