Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamna 17 da za su fafata a zaben 2023 a jihar Kaduna.
Sai dai kuma dan takarar jam’iyyar Labour, Jonathan Asake, sunansa ya bata yayin da aka amince da Alhaji Umaru Farouk Ibrahim a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar.
‘Yan takarar Gwamna a jam’iyyar APC, PDP, da New Nigeria Peoples Party (NNPP); Sanata Uba Sani, Isa Ashiru, da Suleiman Hunkuyi ne suka shiga jerin sunayen.
Sai dai jerin sunayen, sun ruguza tashin hankali da fargabar cewa ba za a lissafa wasu ‘yan takara ba biyo bayan shari’o’in da kotu ta gindaya musu.