Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC, ta amince da sakin dokokin da suka shafi yaƙin neman zaɓe da yawan kuɗaɗen da ƴan takara da jam’iyyu za su kashe a zaɓen ƙasar da ke tafe.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da ilimatarwa kan ƙuri’a na INEC Festus Okoye ya fitar ranar Alhamis, a Abuja.
Okoye ya ce hukumar ta yi taro a ranar ta Alhamis inda ta tattauna kan batutuwa da dama da suka haɗa da wallafa dokokin da suka shafi gangamin yaƙin neman zaɓe, da tarurruka na siyasa da kuma kuɗaɗen da jam’iyyu, da kuma ƴan takara ke kashewa.
Ya ce a yanzu an wallafa bayanai ƙunshi biyu a shafin intanet da shafukan sada zumunta na hukumar, sannan za a raba wa jam’iyyu, da ƴan siyasa, da masu ruwa da tsaki da kuma kafafen yaɗa labaru kwafe-kwafe na bayanan.
Festus Okoye ya kuma tunatar da jam’iyyun siyasa a kan nauyin da ke kansu na miƙa rahoto ga hukumar kamar yadda kundin dokar zaɓe ya tanada.