Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dattawan ƙasar nan.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce, ta gudanar da bikin miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dattawan takardun a babban zauren taro na ƙasa-da-ƙasa da ke Abuja.
A ranar 25 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin ƙasa.