Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta Ƙasa, INEC, ta miƙa wa, Abba Kabir Yusuf, shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.
Abba Kabir, wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u 890,705.
Sai dai kuma har yanzu jam’iyyar APC a Kano, ta ce, ba ta amince da sakamakon zaben ba, wanda ta nemi hukumar zaɓe ta INEC da ta duba lamarin.