fidelitybank

INEC ta magantu a kan katunan zaben da aka binne a Imo

Date:

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta mayar da martani kan wani hoton bidiyo na binne katunan zabe na dindindin, PVC a jihar Imo.

Hukumar a cikin wata sanarwa da kwamishinanta na kasa Festus ya fitar, ta ce ta fara gudanar da bincike cikin gaggawa kuma duk wanda aka samu da laifin aikata hakan za a hukunta shi a karkashin doka.

“An jawo hankalin Hukumar kan faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo na katin zabe na dindindin (PVCs) da ake zargin an binne a karkashin kasa a wasu wurare, ciki har da harabar wani babban kamfani.

“Hukumar ba ta daukar wadannan zarge-zarge da wasa. Mun fara gudanar da bincike cikin gaggawa kuma duk wanda aka samu da laifi a cikin wannan makircin a fili yana da niyyar bata wa ‘yan Najeriya hakkinsa za a hukunta shi a karkashin doka. Duk dan Najeriya da ya cancanta da ya yi rajista a matsayin mai jefa kuri’a, yana da hakkin ya sami katunan zaben.

“Bai kamata a tauye ‘yancin kada kuri’a a kowane zabe ba ko kuma a tauye hakkin tsarin mulki ta kowace hanya.

“Game da tarihin hukumar, an buga katin zabe na PVC ga duk masu rajista a Najeriya har zuwa ranar 14 ga watan Janairun 2022 kuma an kai su ga dukkan jihohin tarayya domin karban masu zabe.

daily post today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp