fidelitybank

INEC ta kulla yarjejeniya da masu motar haya da jirgin ruwa

Date:

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ta kullu wata yarjejeniya tsakaninta da kungiyar motocin haya da masu motocin da na jiragen ruwa, kan yadda za su yi jigila da ma’aikatan hukumar da kuma kayayyakin zabe a lokutan zaben 2023.

Yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan rawar da sufuri zai taka a zabukan da za a gudanar a Najeriya a shekara mai zuwa.

A bangare guda kuma, Tarayyar Turai ta ce za ta aike da masu sa ido kan zaben da aka shirya gudanarwa a ranakun 25 ga watan Fabrairu da kuma na 11 ga watan Maris din 2023.

Yarjejeniyar an kullata ne domin ganin yadda za a kai mambobi da kuma kayayyakin aikin zaben wuraren zaben a kan lokaci kuma cikin aminci.

A yayin kulla wannan yarjejeniya, shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce suna bukatar manyan motoci na haya da kanana har ma da jiragen ruwa domin kai wa ga garuruwan da ke kan hayi.

A cewarsa akwai bukatar mutane sama da miliyan daya da za su yi aikin da motoci sama da 100,000 da jiragen ruwa 4,200 domin yin jigilar kayayyakin aiki zuwa rumfunan zabe 176,846 a mazabu 8,809 cikin kananan hukumomi 774 na jihohin kasar 36.

Irin wannan yarjejeniya aka cimma a ranar 12 ga watan Disambar 2018, domin gudanar da zaben 2019 wanda a cewar shugaban hukumar, nasarar da aka samu ta gudanar da zaben lafiya ta sa aka kara karfafa amfani da hanyar sufurin.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp