Kungiyar ci gaban bil’adama da muhalli (HEDA), ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da ta haramtawa ‘yan takarar siyasa wadanda satifiket din karatunsu ya bata.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar ta HEDA, Olanrewaju Suraju ya fitar ranar Lahadi a Abuja, kungiyar ta ce, ya kamata hukumar zabe ta bi ka’idojin dokar zabe ta 2022 da ka’idojinta tare da bin diddigin ‘yan siyasar da suka yanke shawarar.
Kiran HEDA ga INEC ya biyo bayan wasu ‘yan takarar siyasa a zaben 2023 da suka fito da dalilan da suka sa ba za su iya bayar da satifiket din su ba, da kuma cece-kucen da ake yi na samu, inganci ko akasin haka.
“Muna kira ga INEC da ta yi amfani da tanade-tanaden dokar zabe da ka’idojinta,” in ji sanarwar HEDA.


